Friday, 16 February 2018

Bidiyon ma'aikaciyar Jamb tana fadin cewa maciji ya hadiye miliyan 36 ya bayyana

Matarnan ma'aikaciyar hukumar shirya jarabawar shiga Jami'a wadda labarinta ya karade Duniya inda ta bayyana cewa kudin dake gurinta na sayar da katin jarabawar, miliyan talatin da shida sun bacene saboda hadiyar da wani shu'umin maciji ya musu. Daga baya ta fito ta bayyana CNN cewa sharri aka mata bata ce maciji ya hadiyi kudin ba amma masu iya magana na cewa ramin karya kurarrene domin kuwa bidiyon matar tana bayyanawa masu bincike cewa maciji ya hadiyi kudin ya bayyana.


A hirar da tayi da CNN matar ta kuma ce ba'a binciketa akan batan kudin ba an mikata ga jami'an tsarone kawai, duk wannan maganganu nata yanzu sun zama karya domin jaridar Sun ta samu bidiyon da aka dauka lokacin da ake mata bincike take kuma bayyana cewa maciji ya hadiye kudin.

Domin kallon wannan bidiyo sai a Danna nan

No comments:

Post a Comment