Saturday, 10 February 2018

Buhari Ya Amince Da Gina Hanyoyi Jirgin Kasa Guda Shida

Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi ya bayyana cewa Shugaba Muhammad Buhari ya amince da gina hanyoyin jirgin kasa har guda shida a cikin fadin kasar nan.


Ministan ya ce hanyoyin sun hada da wadda za ta tashi daga Kano-Katsina-Jibiya zuwa garin Maradi da ke Jamhuriyyar Nijar. Sai hanyar Port Harcourt zuwa Maiduguri wadda za ta ratsa garuruwan Enugu, Lafia, Makurdi, Gombe, tare da rassa a garuruwan Owerri, Onitsha, Awka, Abakaliki, Yola, Jalingo da Damaturu.  Sauran su ne na tsawaita hanyar jirgin  Itapke-Aladja (Warri) Uwa Abuja da tashar jirgin ruwa na Warri.
Rariya.

No comments:

Post a Comment