Monday, 19 February 2018

'Buhari yayi abinda babu wani shugaban Najeriya da ya taba yi'>>Cewar Obasanjo a wani yabo da yayiwa Shugaba Buhari

A watan janairu da ya gabatane tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya caccaki shugaban kasa meci, Muhammadu Buhari a cikin wata zungureriyar budaddiyar wasika daya rubuta mishi, a cikin wasikar ya bukaci Buhari da kada ya sake tsayawa takara a zaben 2019 saboda ya gaza.


To amma a wani abu me kama da lashe amanshi da yayi, Obasanjo ya yabi shugaba Buhari akan wani aiki da yace dukkan shuwagabannin kasar da aka taba yi babu wanda ya yishi sai Buharin, aikin kuwa shine, bayar da lasisi kafa kananan matatun man fetur guda ashirin da biyu da gwamnatin shugaba Buharin tayi.

Obasanjo a lokacin da yake kadamar da bude daya daga cikin matatun da wani dan kasuwa ya gina a yankin Neja Delta yace dole ya yabawa Buhari da wannan namijin kokari da yayi duk da cewa shima a lokacin mulkinshi ya bayar da lasisin kafa matatun guda goma sha takwas amma babu wadda aka gida, yawancin wadanda suka amsa sun amsane kawai suyi kasuwanci da lasisin.

Yace amma Buhari ya bayar da Lasisi guda hudu sama da wanda ya bayar, watau guda ashirin da biyu kuma gashi har an gina ta farko a lokacin mulkinshi, saboda haka dole ya yabeshi dan wannan ba karamin abin cigababane.
Leadership

No comments:

Post a Comment