Friday, 9 February 2018

Cikakken bayanin da shugaba Buhari yawa limaman cocin Katolika da suka ziyarceshi jiya: Sun tabbatarmai da goyon bayansu

Jiya, Alhamisne shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mashi bakuncin limaman cocin katolika da suka kaimai ziyara, a sanarwar bayan taro da me taimakawa shugaba Buharin ta fannin watsa labarai, Femi Adesina yayi, ya bayyana cewa shugaba Buharin ya yiwa limaman cocin bayanin cewa maganar ginawa fulani makiyaya gurin kiwo da gwamnatin tarayya ta fito dashi bashi da alaka da mamaya, kamar yanda wasu ke tunani.


Shugaba Bujari ya kara da cewa kamin gwamnati ta fito da wannan tsari saida ta tuntubi masana daban-daban amma da alama wasu sunyiwa abin mumunar fahimta.

Ta bangaren rikice-rikicen dake faruwa a jihohin Benuwe da Adamawa da Zamfara da Taraba kuwa shugaba Buhari yace, ba daidai bane ayi tunanin wai yana ofis cikin na'urar sanyaya daki be san abinda ke faruwa ba, yace yayi jagorancin bangarori uku cikin hudu na sojoji da ake da su a kasarnan lokacin yana aikin soja, saboda haka suna sane da abinda yake faruwa kuma suna daukar matakin daya dace.

Ta bangaren tsaro kuwa shugaba Buhari yace an samu cigaba sosai, musamman idan aka duba Arewa maso gabashin kasarnan inda yakin Boko Haram ya daidaitashi, yanzu an samu sauki ba kamar yanda suka iske yanayinba.

Ta bangaren tattalin arziki kuwa shugaba Buhari yace mutanen Najeriya da dama sun amshi tsarin da gwamnati ta fito dashi na harkar noma kuma sun ji shawarwarin da aka basu, da yawa suna darawa yanzu saboda sun ci ribar abin.

Ta bangaren rabon mukaman gwamnati shugaba Buhari yace babu wani bangare na rabon mukamai da aka nuna sonkai a ciki da gangan amma ya bayyana cewa idan aka kawo mai cikakken bayanin yanda rabon mukaman yake, zai duba yaga irin korafe-korafen da ake yi akai.

Ta bangaren yaki da cin hanci da rashawa kuwa, shugaba Buharu yace duk ma'aikacin da aka sameshi da yin ba daidai ba musamman wajan dibar dukiyar al'umma kuma aka samu kwararan shedu to za'a gurfanar dashi gaban kuliya dan yi mishi hukuncin daya dace.

A karshen ganawar tasu limamin cocin daya wa limaman jagora zuwa fadar gwamnati, Ignatious Kaigama ya bayyana cewa cocin katolika zata cigaba da baiwa gwamnatin shugaba Buhari goyin baya da kuma bayar da gudummuwarsu wajan gina kasa ta hanyar addu'o'i.

No comments:

Post a Comment