Saturday, 10 February 2018

Dalilan da ya sanya na ke son kauracewa duk wani gangami na yakin neman zaben 'yan takarkaru a siyasar 2019.

Wannan bawan Allahn ya bayyana dalilin daya sa bazai je wani taron siyasa ba nan gaba kamar haka:

1-Duk lokacin da za a tafi gangamin yakin neman zabe za ka ga babu 'ya'yan wadannan 'yan takarkaru a cikii.

2- Kafin a kafa gwamnati zaka ga 'ya'yan talakawa sune sahun gaba, amma da zaran an kafa gwamnatin za ka 'ya'yan talakawa sun koma sahun baya.3- Haka kuma duk wasu ayyuka masu mahimmaci a gwamnati, za ka ga ba a saka 'ya'yan talakawa, in kaga an neme su aikin wahala ne.

4- Haka kuma na lura kashi 80% masu bangar siyasa, siyasa 'ya'yan talakawa ne, idan abin kikirki ne, me ya sanya wadannan 'yan takarkar basu sanya 'ya'yansu ?

5- Ta ya ne zanje in rasa rayuwata akan kare neman duniyar wani ? Sabanin 'ya'yansu ba za su shiga ba, suna can kasashen waje suna karatu.

Don haka a shirye na ke da in kauracewa duk wani gangami na yakin neman 'yan takarkaru a 2019, saboda naga mafi yawan  'yan siyasa boye 'ya'yansu suke yi a lokacin yakin neman Zabe.

No comments:

Post a Comment