Thursday, 15 February 2018

Dalilin fadana da kwankwaso: Yana so ya juyanine ni kuma na kiya>>Gwamna Ganduje

A wata ganawa da yayi da manema labarai, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yayi bayanin dalilin rikicin dake tsakaninshi da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, inda yace Kwankwason naso ya rika juyashine ta hanyar gayamai abinda zai yi, shi kuma yaki lamuntar hakan.

Ganduje yace tarihin rayuwar siyasarshi baza ta kammalu ba idan babu Kwankwaso, haka shima Kwankwason tarihin siyasarshi dole a sako Gandujen a ciki, amma akwai lokacin da a matsayinshi na gwamna be kamata ace wanine zai rika juyashi ba.

Haka kuma Gandujen yayi bayani akan zaben kananan hukumomi da akayi a Kano inda aka rika watsa hotunan kananan yara suna kada kuri'a, Gwamnan yace ba gaskiya bane, mutanen yanar gizo ne kawai suka hada abubuwansu amma zaben kananan hukumomi anyishi cikin tsafta da tsari me inganci kuma koda masu saka iso a harkar zabe sun shaida hakan.
Leadership.

No comments:

Post a Comment