Monday, 5 February 2018

Dambarwa na neman barkewa a masana'antar fina-finan Hausa: Ali Nuhu yace kada wanda ya zagi wani saboda shi

Da alama akwai wata dambarwa dake faruwa a masana'antar fina-finan Hausa, domin kuwa a jiyane mukaji labarin Bello Muhammad Bello(General BMB) an kaishi bango yana zage-zage, inda yayi zargin cewa an turomai yara suna mai rashin kunya, haka kuma yau munji labarin Adam A. Zango shima ya fito da wani sabon shirin gyara a masana'antar, duk dadai yace ba da Ali Nuhu yake yi ba.Ali Nuhun ya fito ya nuna halin dattako ya bayyana cewa" ina rokon duk masoyana maza da mata duk wanda ya san tsakani da Allah yake so na ya daina saka labari dan cin mutuncin wani ko wata. Bana rigima ko batanci ga duk wani abokin sana'ata sannan duk wanda ya yi min ku barshi da Allah. Babu sakayyar da ta wuce ta Allah"
Har yanzu dai ainihin abinda ya jawo wannan cece-kuce be bayyana ba, ama dai koma mene muna fatan Allah ya sa a daidaita.

No comments:

Post a Comment