Tuesday, 27 February 2018

Dan shugaban kasa, Yusuf Buhari ya dawo Najeriya bayan jiyyar da yayi a kasar waje

Bayan kulawar da ya samu a asibitin kasar waje dalilin ciwon da ya ji a hadarin babur da ya ritsa dashi, dan shugaban kasa, Yusuf Buhari ya dawo gida Najeriya a daren jiya Litinin kamar yanda rahotanni ke nunawa.


Jaridar Thisday tace ta samu labarin dawowar ta Yusuf Buhari a daren jiya kuma ga dukkan alamu ya samu sauki sosai, saidai bata samu labarin ko wace kasa ce yaje kwanciyar asibitin ba.

Muna fatan Allah ya kara mai lafiya da sauran 'yan uwa marasa lafiya dake asibiti da gidaje.

No comments:

Post a Comment