Sunday, 4 February 2018

DAN TALAKA, KAI BA JAKI BA KUMA KAI BA MANGALA BA: Ahirr dinka wallahi da rikicin siyasa


Image may contain: 7 people, people smiling, people standing

Ina so duk dan talaka da yake yin sara-suka saboda 'yan siyasa ya amsa wadannan tambayoyin guda goma sha biyar :-
1. Menene ribar da ka samu tsawon lokacin da ka yi a cikin jagaliyar siyasa?
2. Wai ka taba zuwa Abuja ka ga rayuwar da suke yi da su da 'ya'yansu?
3. Shin sun taba tunanin mayar da kai makaranta?
4. Ka fi 'ya'yansu son su ne da ba za su fito a yi arangama da su ba?
5. Dama Allah ya halicce ka ne don ka bautawa wani?


6. Wani a cikinsu ya taba yi maka nasiha akan ibada ko rayuwarka?
7. Kana tunanin makomar rayuwar gidanku kuwa?
8. Ka gane cewa ba su da bukatarka sai zabe ya zo?
9. Kana da gado ne a cikin dukiyarsu?
10. Ka cire rai da arziki ne kai?
11. Baka sha'awar ka hau kujerar da suke kai?
12. Ka san kuwa suna sane suka bar ka da jahilci?
13. Kana iya cin lafiyayyen abinci sau uku a kowacce rana?
14. Ka taba tunanin cewa kullum kara tsufa kake yi su kuma kara samun duniya suke?
15. Ka yadda cewa Soron-dinki talaka ne masoyinka?
Wadannan tambayoyin guda goma sha biyar sun ishe ka ka yi wa kanka hisabi, za ka gane hadarin da rayuwarka ta dosa. Mafi munin abun shine kai dai ba karatu bane da kai balle su baka aiki kuma kai ba nutsuwa bace da kai balle su baka kwangila ko jari. Ka ga ka zama kai ba JAKI ba kai kuma ba MANGALA ba.
Allah ya shiryar da mu.
Daga Sheik Yusuf Sambo Rigachikun.
rariya.

No comments:

Post a Comment