Saturday, 17 February 2018

Dan wasan Liverpool Muhammad Salah ya sanyawa turawa da yawa son Musulunci

Irin salon kwarewar wasa da nuna hazaka ta Muhammad Salah, wanda ya fito daga kasar Misra/Egypt kuma yake bugawa kungiyar Liverpool ta kasar Ingila wasa yasa masoyan kungiyar, turawa suka nuna sha'awar shiga musulunci.


An ruwaito dubban magoya bayan kungiyar suna rera wakar cewa suna son Muhammad Salah kuma idan ya kara cin kwallaye nan gaba to zasu musulunta haka kuma sun kara da cewa, idan ya shiga masallaci muma zamu bishi mu zauna tare dashi.

Moh Salah yana kara samun amsuwa sosai a gasar Firimiya ta kasar Ingila, dan shekaru 25 yana bugawa kasarshi wasa kuma shine ya lashe kwarzon dan kwallon BBC na Afrika na shekarar 2017 data gabata, a ranar Larabar data gabata, Muhammad Salah ya shiga cikin 'yan wasan kungiyar Liverpool 13 kacal da suka taba cin kwallaye 30 a kakar wasa, wasu ma har suna hada kwarzan takarshi da dan wasan Barcelona Lionel Messi.

Wannan abu daya faru ya matukar birge mutane inda da yawa suka yi ta yabawa da Muhammad Salah din kuma wasu sukayi hasashen cewa soyayyar Muhammad Salah zata rage yawan kiyayyar da akewa musulmi da kuma wariyar launin fata.

Muna mishi fatan Alheri da fatan Allah ya kara daukakashi.

No comments:

Post a Comment