Tuesday, 27 February 2018

Dangote ya hana a kawo giya gurin bikin diyarshi

Rahotanni daga gidan me kudin Duniya, Aliko Dangote na cewa ya hana a kawo giya gurin bikin diyarshi Fatima da zai aurawa, dan gidan tsohon shugaban 'yan sanda Jamil MD Abubakar.Shagalin bikin dai da rahotanni suka nuna an tsara cewa za'a yishi a kasaitaccen otaldin Eko dake Legas wanda kuma zai samu halartar manyan mutane da suka hada da me kudin Duniya, Bill Gates.

Dama dai musulunci ya hana mu ta'ammali da barasa, muna fatan Allah yasa ayi lafiya.

No comments:

Post a Comment