Sunday, 4 February 2018

Dangote zai aurar da diyarshi, Fatima ga dan gidan tsohon shugaban 'yan sanda, Jamil MD Abubakar

Hamshakin attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote zai aurar da diyarshi, Fatima ga dan gidan tsohon shugaban 'yansandan Najeriya, MD Abubakar watau Jamil, auren nasu wanda rahotanni daga Capital.ng suka bayyana cewa za'a daura a watan Maris me zuwa zai samu halartar manyan mutane daga ciki da wajen kasarnan.Jamil matukin jirgin sama ne a yayin da ita kuma Fatima babbar ma'aikaciyace a kamfanin yin kek na "Cup Cake Factory", cikin wadanda ake tsammanin zasu halarci shagalin bikin da za'ayi a otal din Eko dake Legas hadda attajirin me kudin Duniya, Bill Gates da kuma shuwagabannin kasashe daban-daban da tsaffin shugabannin kasa na Najeriya dadai sauran manyan mutane masu kumbar susa.No comments:

Post a Comment