Thursday, 8 February 2018

Dubai ya kawo wasu bishiyoyi masu ban al'ajabi dake yiwa waya caji da kuma bayar da damar shiga yanar gizo

Smart palm: At night the trees discharge energy and WiFi for 100 metres
Garin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa yayi suna a Duniya wajan kasuwanci da abubuwan kayatarwa na more rayuwa kala-kala dake jan hankulan dukan mutanen Duniya, daga kasashe daban-daban suna zuwa yawon shakatawa acan, wannan karin shima wani abin kayatarwane da daukar hankali da Dubai din ta kawo. Bishiyoyine masu kama da na dabino akayi, amma aikinsu shine su rika caja wayoyin mutane da kuma basu damar shiga yanar gizo.


One of the first Smart Palm trees has been installed on the beach front near to the Burj Al Arab in Dubai
Bishiyoyin dai ba irin wadanda muka san ana dasawa bane su girma, a'a wadannan na'urorine akawa siffar bishiya dan su kayatar, kuma suna da fuskar da zata nuna maka abinda kake yi, misali, kamar fuskar waya ko talabijin, haka kuma bishiyoyin sun amfani da hasken ranane. Da rana zasu zuki haske ya musu caji, da dare kuma zasu baiwa mutane dama suyi cajin wayoyinsu dasu sannan kuma su basu damar shiga yanar gizo a kan iska.
UAE sun: Solar panels soak up energy during the day at the Smart Palm installed at the Dubai park
A yanzu dai an kafa bishiyoyin masu ban al'ajabi guda biyu a binin na Dubai kuma kamfanin dake aikin kafasu yace zasu kafa guda ari da ukune a sassa daban-daban na birnin. za'a kafa bishiyoyinne a guraren shakatawa da bakin ruwa, inda mutane ke zuwa hutawa da yamma, kowace bishiya na da gurin yin caji guda takwas, kuma kamfanin da ya hadasu yace karfin cajin da zasu ba wayoyi, ya ninka wanda cajar mutum zata bashi sau biyu da rabi.
The ceremony launching the Smart Palms was well attended by UAE locals
Da rana za'a iya zama karkashin bishiyar dan samun inuwa, da yamma kuma ayi amfani dasu wajan shiga yanar gizo da yin caji. Hmmm Duniya na ta kayatuwa.
Smart Palm tree launched the new technology in a special ceremony in Dubai

Night life: Beach goers flock to see the new arrival on the Surf Beach
Dailymail-UK


No comments:

Post a Comment