Monday, 5 February 2018

"Duk wani Jarumi dana taba kyautata mishi ina so ya fito ya gayawa Duniya: Idan ba haka ba bazai kara cin moriyata ba">>Adam A. na Shirin kawo gyara a masana'antar fim din Hausa

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya fito da wani salon gyara, kamar yanda ya kirashi a masana'antar fina-finan Hausa, Adam yace yana so masoyanshi a cikin masana'antar tasu su fito su nuna irin soyayyar da suke mishi a fili kada suji tsoron kowa.Adamun ya kara da cewa duk ya taba yiwa abin Alheri ya fito ya fada kada ya ji tsoron cewa wai idan ya fada wani zai daina sakashi a fim dinshi, yace, ka yarda Allahne ke bayarwa, yace bawai alherinshi kadaiba, yana so a fadi hadda sharrinshi yana so a bayyana domin gayara yake nema kuma yana so a fara daga kanshi, a karshe Adamu yayi barazanar cewa duk wanda be fito yayi hakan ba to ya fita daga Haularshi(wata kila yana nufin baya tare dashi ko kuma bazai sake taimakonshiba). Adamun yace be damu ba ko da za'ace wai Riyace yayi.

Adamun ya fara da kanshi inda ya lissafo mutanen da ya bayyana su a matsayin tushenshi.


"IDAN ZA'AYI GYARA WANI LOKACIN DOLE SAI ANYI BARNA!
SALISU MU'AZU
IBRAHIM DANKO
BELLO IBRAHIM
ADAM M. ADAM
NAZIRU HAUSAWA
NAJASHI SB JAKARA
FALALU A. DORAYI
YAKUBU MOH'D
ALI NUHU
BABAN CHINEDU
SADI SIDI SHARIFAI
ABUBAKAR SANI
MUSBAHU M. AHMADA
LAWAN KAURA
SULAIMAN SA'EED
HAUWA M.D
MARYAM MASHHAMA

WADAN NAN SUNE TUSHEN A. ZANGO KUMA BAN TABA BOYEWA BA KUMA BAZAN TABA MANTA BA."

Adamun yayi karin bayani akan wannan gyara da yake so yayi in da yace, shi ba da Ali Nuhu yake fada ba, a'a yana fadane da wadanda suke zaluntar jarumai su musu aiki basa biyansu hakkinsu yanda ya kamata kuma su jaruman suna jin tsoron kada suyi magana, gobe aki sakasu a fim. Adamun ya bayar da misali inda yace wasu zasu je gurin sabbin produsoshi daga waje su amso kudinsu su cucesu, ko kuma su saka kudi kada da basu wuce dubu dari biyar ba akan fim har a gamashi kuma da manyan jarumai a ciki.
Adamu yace wannan abu da ya fara yasan cewa akwai hadari domin har rayiwarshi za'a iya nema amma ya sadaukar da ranshi dan kawo gyara.

Tuni dai har wasu daga cikin jaruman da suka hada da Fati Shu'uma sun fara bayyana Alkhairan Adamun.


No comments:

Post a Comment