Thursday, 8 February 2018

Dusar kankara ta sake zuba a Saharar kasar Aljeriya

Ikon Allah ya wuce mamaki, a farkon shekararnanne mukaji labarin yanda dusar kankara ta zuba a saharar kasar Aljeriya, abinda yayi ta baiwa mutane mamaki duk da cewa shekaru arba'in da suka wuce hakan ta tafa faruwa, a ranar talatar da ta gabata sai gashi kuma dusar kankarar ta sake zuba a kasar da Aljeriya dai.Dusar kankarar ta rufe yashin dake garin da ta sauka inda yayi fari fat, gwanin ban sha'awa, yara da manya sun fito suna kallo kuma sun dauki hotuna. Wasu dai sun rika danganta wannan lamari da cewa rikicewar yanayin Duniyane wasu kuma sukace ai alamar karshen Duniyane, abinda ake ganin bazai faru ba gashi yana faruwa.

Dailymailuk

No comments:

Post a Comment