Thursday, 15 February 2018

"Gimbiyar mata kawai ake haifa a rana me kamar ta yau": Ummi Zeezee na murnar zagayowar ranar haihuwarta

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Ummmi Zeezee na murnar zagayowar ranar haihuwarta a yau, Alhamis, 15 ga watan Fabrairu, Ummi ta bayyana cewa, Gimbiyar mata kawai ake haifa a irin wannan ranar kuma ita tayi sa'a an haifeta a rana me kamar ta yau din, saboda haka ta na taya kanta murnar zagayowar ranar haihuwarta.Muna taya Ummi murna da fatan Allah ya karo shekau masu albatka.

No comments:

Post a Comment