Thursday, 22 February 2018

Gwamna Fayose ya gaisa da shugaba Buhari: 'Yan Najeriya suna ta magana akai

A yaune shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar manyan kasarnan data hada da tsaffin shuwagabannin kasa da gwamnonin kasarnan kaf da tsaffin masu shari'a da shuwagabannin majalisun tarayya, wani abu daya dauki hankulan mutane sosai a wannan taron shine gaisuwar shugaba Buhari da gwamnan jihar Eikiti, Ayodele Fayose.Gwamna Fayose dai yayi kaurin suna wajan caccakar shugaban kasa, Muhammadu Buhari harma da iyalanshi amma da alama kuma yana so shugaba Buharin ya kulashi, domin kuwa koda a lokacin da yayi murnar zagayowar ranar haihuwarshi saida yayi ta fafatu cewa wai shugaba Buhari be tayashi murna ba.
Duk da irin wadancan abubuwa da Fayose yakeyi shugaba Buhari be taba kulashi ba, sai gashi yau sun hadu.

Wani abinda ya kara daukar hankulan mutane a wannan taro shine haduwar shugaba Buharin da tsohon shugaban kasa, Olusegun obasanjo wanda shima har takarda ya rubutawa shugaba Buharin akan kada ya tsaya takarar shugaban kasa, duk da cewa a 'yan kwanakinnan ya dawo yana yabon gwamnatin ta Buhari.

No comments:

Post a Comment