Thursday, 1 February 2018

Gwamnatin Shugaba Buhari zata gina matatar mai a jihar Katsina

A jiyane, karamin ministan albarkatun mai, Emmanuel I. Kachiku ya kai ziyara jamhuriyar Nijar inda ya gana da shugaban kasar, Muhammadou Issufou aka kuma yi alkawarin gina mamatar mai a wani gari dake cikin jihar Katsina kan iyakar Najeriya da Nijar.Haka kuma za'a ajiye bututu da zai rika kawowa matatr man man da zata rika tacewa daga jamhuriyar Nijar din. Nan gaba kadan za'a sakawa takaddun alkawarin hannu.
Dalilin gina bututun mai da kuma hanyar jirgin kasa daga Najeriya zuwa Nijar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi alkawarin yi a jawabinshi na sabuwar shekara, ya fara fitowa fili, muna fatan Allah ya kara taimakon shuwagabanninmu aka  ayyukan Alheri da sukeyi.

No comments:

Post a Comment