Monday, 12 February 2018

"Hausawa/Musulmai mutanen kirkine: Basa zambatar mutum"

Wannan baiwar Allahn, wadda ga dukkan alamu daga kudancin kasarnan take ta yabi Hausawa/musulmai dalilin hali na gari da wani Bahaushe ya nuna mata, tace, Hausawa na da Matukar gaskiya, baza su iya zambatar mutum ba.Dalilin ta kuwa shine, kamar yanda ta bayar da labari, ta aika katin dubu biyu ga wata lambar da bata sani ba bisa kuskure, sai ta kira lambar, taji Bahaushene, ta mai bayani, sai ya mayar mata da katinta, ta kara da cewa hadda bata hakuri yayi.

Abindai ya birge, amfani Hali na gari kenan a duk inda mutum ya samu kanshi, zai jawowa kanshi kima, 'yan gidansu, danginshi, addini, dama al'ummar da ya fito daga cikinta

No comments:

Post a Comment