Thursday, 15 February 2018

Hukumar soji ta saka tukwicin miliyan 3 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kama shugaban kungiyar Boko Haram

Hukumar soji ta kasa ta fitar da sanarwar bayar da tukwicin zunzurutun kudi har naira miliyan uku ga duk wanda ya bayar da bayanan da zasu kai ga kama shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, hukumar sojin ta bayyana Shekau a matsayin wanda ya tsere ya kuma ke neman mafaka dan gujewa kamun jami'an tsaro.


Sanarwar tayi karin bayanin cewa idan mutum nada bayanin inda Shekau din yake yana iya sanar da rundumar Lafiya Dole dake Borno  ko kuma wata hukumar soji mafi kusa dashi, za'a baiwa duk wanda ya kawo wannan bayani tsabar kudi, ba cek ba, babu jeka ka dawo, naira miliyan uku.

No comments:

Post a Comment