Sunday, 4 February 2018

IBB ya shawarci shugaba Buhari da ya hakura da mulki ya mikawa matasa

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya aike da wani rubutaccen sakon ga shugaba Buhari inda yake shawartar sa da ya hakura da batun takarar shugabancin kasa a zaben shekarar 2019.


A wani jawabi da IBB din ya fitar a yau, Lahadi, ya bayyana rashin gamsuwar sa ga salon shugaba Buhari da ma jam'iyyar APC bakidaya.

Kazalika, ya goyi bayan yin garambawul ga tsarin mulkin Najeriya, musamman a bangaren rabon iko a tsakanin bangarorin gwamnati.

Babangida ya bayyana takaicinsa na gaza samun shugaba nagari a Najeriya da zai kawo canji na hakika a kan yadda al'amuran kasa ke gudana tare da shawartar Buhari cewar "lokaci ya yi da ya kamata ya ajiye bukatar kansa ya rungumi kishin kasa ta hanyar fasa tsayawa takara a zabe mai zuwa."

"Bisa ga yadda al'amura ke gudana, akwai bukatar mu goyawa shugaba Buhari baya ya kammala zangon mulkinsa da zai kare a watan Mayu, 2019 tare da hada kai da shi domin fitar da matashi daga cikin 'yan Najeriya da zai maye gurbinsa," A cewar Babangida, mutumin da ya mulki Najeriya daga shekarar 1985 zuwa shekarar 1993.

Jawabin na IBB ya cigaba da cewar "Ina bayar da wannan shawara ne a matsayina na mai ruwa da tsaki a sha'anin mulkin Najeriya, a matsayina na tsohon shugaban kasa, da kuma dan kishin kasa dake son ganin kasar sa hau hanya madaidaiciya da zata tabbatar ta cigaba mai dorewa. Ina so jama'a su sani cewar, don na bayar da shawara, hakan ba yana nufin ina son yin kutse cikin 'yancin Buhari na tsayawa zabe ba kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya sahale masa, illa iyaka dai na san akwai lokaci da a rayuwa ya kamata mutum ya jingine bukatar kashin kansa domin inganta rayuwar kasar sa."

Wannan sako na Babangida na zuwa ne sati guda kacal bayan wasikar da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya aikewa Buhari yana shawartar sa da a'kul ya sake ya fito takarar shugabancin Najeriya a zaben 2019, kamar yadda jaridar Naij.com ta rawaito maku.
naija.ng


No comments:

Post a Comment