Saturday, 3 February 2018

"Idan aka mareka ka juya dayan kuma tun">>Gwamnan jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad a wani sako da ya fitar ta dandalinshi na sada zumunta, ya bayyana cewa su ba masu tashin hankali bane kuma yana rokon cewa kada masu goyon bayanshi su yi fada, koda wani ya mare ka juya mishi daayan kumatun.Ga abinda ya fada kamar haka:
"Ina hada ku da Allah kar ku zagi kowa, kar ku yi fada da kowa, kar ku tsokana kowa, mu ba ma su neman tashin hankali ba ne. In wani ya mare ka, kar ka rama, ka ma juya masa daya kumatun don dai a zauna lafiya."

No comments:

Post a Comment