Friday, 23 February 2018

INA MAI NEMAN TSIRA GOBE KIYAMA>>Fadakarwa daga Dr. Tukur Adam Almanar

Wani mutum ya rubuta takarda zuwaga Abdullahi Dan Umar, - Allah Ya yarda da su-, cewa ya rubuta masa dukkan ilimi....

Sai ya rubuta masa cewa, lallai ilimi yana da yawa, amma idan zaka iya gamuwa da Allah:
-baka da nauyin hakkin jinin mutane a wuyanka...
-mai tsare cikinka daga cin dukiyansu ta hanyan haram...
-Mai kame harcenka da tsare shi daga cin mutuncinsu...
-Mai lizimtan hadin kansu ba, to ka aikata..

Siyaru A'alamin Nubala'i na IMAM Zahabi Allah masa rahama 5/216.

Allah Ka tsare mu daga zubar da jinin wani, da cin dukiyar haram, da cin mutuncin wani, da raba kan Al'umma..

No comments:

Post a Comment