Wednesday, 7 February 2018

"Jahilai da basu da ilimin addini cikin masoya Buhari ke yin zagi in an sokeshi: Amma masu Ilimin addini shiru sukeyi dan sun san gaskiya ake fadi">>Ummi Zee

A satin daya gabatane tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa ta shiga kanun labarai bayan datayi suka akan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da dama sun mayar mata da kakkausan raddi, wasu har dandalinta na sada zumunta suka bita suna mayar mata da martani.A nan wanine daya je har dandalin Ummin yake mata raddi akan sukar da ta yiwa shugaba Buharin, Umminn ta mayar mishi da martanin cewa, ai masu ilimin addini cikin masoyan shugaba Buharin idan an zageshi shiru sukeyi saboda sunsan abinda ake fada akanshi gaskiyane, jahilai sune ke zagi"

Ummin ta kara da cewa sai Allah ya tambayi Buhari saboda irin wahalar da ya saka mutanen kasarnan a ciki, "mutane na kwana da yunwa dalilin mulkinshi" duk hakkin gana kanshi.

No comments:

Post a Comment