Monday, 26 February 2018

Jarumar Fim din Indiya, Dipika ta musulunta

Wata jarumar fina-finan Indiya me suna Dipika Kakar ta amshi addinin musulunci, an danganta musuluntar tata da cewa, sanadiyyar wanda ta aurane me suna Shoaib Ibrahim, a jikin katin Gayyatar aurensu anga Dipikar ta canja suna zuwa Fa'iza.Dunya News sun ruwaito cewa an daura auren masoyan a gidan mijin , watau Shoaib Ibrahim inda 'yan uwa da abokai suka halarta, muna fatan Allah ya sanya albarka a wannan aure nasu ita kuma muna mata fatan Allah ya kara mata fahimtar addini.

No comments:

Post a Comment