Sunday, 25 February 2018

Jarumar fina-finan India Sridevi ta rasu

Fitacciyar jarumar fina-finan Bollywood Sridevi Kapoor, ta rasu a daren ranar Asabar sakamakon bugun zuciya. Kanin mijin jarumar, Sanjay Kapoor, shi ne ya tabbatar wa da manema labarai na India labarin mutuwar ta, inda ya ce ta mutu ne Dubai, bayan sun je biki tare da mijinta Boney Kapoor da kuma 'yar ta Khushi.


An dai haifi Sridevi ne a ranar 13 ga watan Augustan shekarar 1963 a Tamil Nadu.
Sridevi ta fara fitowa a fina-finan Tamil ne tun tana karama wato tana da shekara hudu a duniya , amma a shekarar 1975 ne ta fito a fim da girmanta wato fim din Julie, daga nan ne ta ci gaba da fitowa a fina-finai amma na Tamil.

Fim dinta na farko da ta yi wato na Hindi shi ne fim din Solva Sawan wanda aka yi shi a shekarar 1979.
Shekara hudu bayan nan kuma sai aka hadata fim da Jeetandra wato fim din Himmatwala wanda kuma ya yi matukar fice a shekarar da aka sake shi wato 1983. Daga nan ne fa Sridevi ta koma fitowa a fina-finan Hindi.

Tayi fina-finai fiye da 150 ciki har da wadanda da suka yi fice kamar, Mawali da Sadma da Mr India da Chandni da Nagina da Chalbaaz da Janbaaz da English Vinglish da Chandra Mukhi da kuma fim din ta na karshe da ya fita bara wato Mom.

Ta rasu ta bar mijinta da 'ya'ya mata biyu wato Jhanvi da Khushi Kapoor. Sridevi ta bayar da muhimmiyar gudunmuwa a fina-finan Bollywood. Ta karbi lambobin yabo da dama bisa rawar da ta taka a fina-finan. Tana daga cikin jarumai mata da suke da kyau sosai, da kuma iya rawa.

Ta fara auren jarumi Mithun Jakraborty ba su haihu ba, daga baya kuma ta auri mai shirya fim da bayar da umarni Boney Kapoor, inda suka haifi 'ya'ya biyu mata Jhanvi da Khushi Kapoor.
Tuni jarumai irinsu Priyanka Chopra da Reteish Deshmukh da Sharukh Khan da sauransu suka 

wallafa alhininsu bisa rasuwar jarumar a shafukan sada zumunta.
bbchausa

No comments:

Post a Comment