Thursday, 8 February 2018

Jihar Kaduna ta tura dalibai 60 kasashen waje karatun kiwan lafiya

Gwamnatin jihar Kaduna, karkashin jagorancin gwamna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ta dauki nauyin karatun wasu dalibai guda sittin zuwa kasashen wajen dan karantar harkar kiwaon lafiya. Talatin daga cikinsu zasu je kasar Uganda ne yayin da sauran talatin din kuma zasu je kasar Cuba.
Gwamnan ya bayyana cewa, ya gana da daliban yau a gidan gwamnati kamin su tafi guraren karatun nasi inda ya hore su da su zama wakilai na gari su kuma jajirce su yi karatu yanda ya kamata.
No comments:

Post a Comment