Sunday, 11 February 2018

Kalli Garin da ba Maza sai mata

Wata mata me suna Kristina Roth ta bude wani tsibiri inda tace matane kawai zata baiwa damar zuwa gurin,matar tace ta lura da irin yanda mazake sanya mata su rika yin abu dan su birgesu shiyasa ta bude wannan guri domin baiwa mata dama su lura da kansu su kuma baiwa kansu muhimmanci bawai kokarin birge wani ba.

Kristina ta bude wanna gurine a kasar Finland kuma ya zuwa yanzu ita kadaice da kawayenta suke zaune a wannan tsibiri amma tace nan da watan Yuni na wannan shekarar zata baiwa sauran mata masu sha'awar zuwa wannan guri domin su hadu da sauran mata 'yan uwansu su tattauna matsalolinsu na mata.

Ta kara da cewa bawai ta tsani maza bane, watakila nan gaba ma ta baiwa maza damar zuwa wannan gari nata amma yanzu tana so ta baiwa mata wani yanayine na maida hankali kan rayuwarsu.
Independent/uk

No comments:

Post a Comment