Tuesday, 13 February 2018

Kalli sakon barazana da yaron wani babban jarumin fim din Hausa ya turawa Nura M. Inuwa

Tauraron mawakin Hausa, Nura M. Inuwa ya bamu labarin sakon da wani ya aikamai wanda yace yaron wani babban jarumine a masana'antar fina-finan Hausa inda yace an gayamai cewa wai zasu zo su ida aikinsu na watsamai Acid da sukayi. Nira yayi alkawarin nunawa Duniya sakon da aka aikemai din kuma ya cika alkawarinshi.Ga hoton sakon da aka aikewa Nura nan a kasa kuma ya bayyana cewa baya jin tsoron kowa sai Allah.
Bayan saka wannan sako Nura yayi bayani kamar haka:
"Wannan shine sakon da aka turamin tun kafin ince komai bana nufin kowa da sharri duk masoyina yasan haka bana kokarin gani bayan kowa kuma bansan me yasa suke son ganin nawa ba inada makiyan boye inada na fili wanda duniya ta sani ban kuma san abin danayi musu ba sama da shekaru shida duk wanda ya damu dani sai sunyi kokarin rabani dashi hakane ma yasani fahimtar masoyana suna nesa dani sune wadan ba a sansu bare a hure musu kunne ko ayi musu barazana sau da yawa nakan zauna nayi kukan abin da akemin musamman na nunawa mutane ban kai asoniba da akeyi ko kuma a dauki gaba da wanda yake sona batare da dalili ba duk da kokarin ku na hana mutane bani aiki da kukeyi ALLAH bai hanani ba in mutum ya yabeni ku zageshi inya dora hotona kirashi kuce ya cire duk akan me ? toni dama ban dorawa kaina kowa za soni ba wanda kuke da iko dasu ku hana su sona ku hana wanda kuma baku da iko kuyi rayuwata da mutuwata bata hanun kowan ku in kuma kunyi nasarar kasheni ku ku gaji duniya ina tare da masoyina duk inda yake zanci gaba da fadawa duniya duk abin dana boye a zuciyata."

Allah shi kyauta.

1 comment:

  1. Subhanallah, Nura Allah ya fi su, Allah shi ne mai daukakawa kuma shi ne mai kaskantarwa, saboda haka, ai ba da kai suke yi ba, da Allah ne su ke rigimar. Ku kuma ma su neman bayar Nura M. Inuwa, mai ya yi zahi haka? Shin kushe ne maganin wanda Allah ya dora shi a kan ka ko kuma neman hazaqa? Wallahi tallahi, wannan ba mahuta ce gare ku ba, tun wuri ku nemi yapiyar sa da ta Ubanguigi wataqila ko za ku gama lahiya. Ko kuna fahimtar ku za ku dore zaman duniyar ne ba za ku mace ba????? Allah ya wadarn naka ya lalace wai raqumin dawa da ya ga na guida dawke da kaya!!!

    ReplyDelete