Monday, 26 February 2018

Kalli yanda mahaifi ya daure danshi a jikin babur dan ya kaishi makaranta

Wannan wani hoto ne dake ta yawo a shafukan sada zumunta da rahotanni suka bayyana cewa irin yarannanne masu kyuyar zuwa makaranta, shine mahaifin nashi ya daureshi da danko a bayan babur dan ya kaishi makarantar.


Wasu dai na ganin hakan cin zarafin yaronne inda har suke kiran masu kare hakkin bil'adama su kawo dauki amma da yawa kuma sun yaba da wannan abu tunda ilimi shi zai yiwa mutum jagora a rayuwa wajan sanin abinda ya kamata.

No comments:

Post a Comment