Saturday, 24 February 2018

Kalli yanda Mutane suka daka wawa akan kudin da Atiku ya basu a filin jirgin saman Kano

Wasu rahotanni na cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar yaje jihar Kano, inda ya raba kudi a filin jirgin saman, kuma wadannan hotunan da ake gani, yanda mutane, ciki hadda wasu ma'aikatan gurin ke wawar kudin da Atikun ya bayar kenan.Lallai kam shiyasa 'yan siyasarnan sun san lagon talaka, zasu bari sai suna neman abu a hannunshi sannan su rika watsa mishi tsaba yana tsatstsaga, Allah shi kyauta.

No comments:

Post a Comment