Friday, 16 February 2018

Kalli yanda wannan mutumin ya hada kwallon ashana

Wani mutum me suna Wallace dan kasar Amurka ya hada kwallon Ashana ta hanyar manne kwayoyin ashana da yawansu yakai dubu arba'in da biyu guri guda da gam har suka bayar da siffar kwallo, watanni goma a kwashe yana yana wannan aikin kamin ya samu nasara.

Mutumin yace yana zaunene kawai yana wasa da Ashana sai tunani ya zo mishi cewa watakila idan hada ashana da yawa guruoi guda zasu bashi siffar kwallo, daga nan ya tashi ya gwada ya gani cewa idan ya hada kan ashana guda biyu ta kasa suna matsewa ta sama kuma suna budewa, hakan ya battar mai da cewa burinshi zai iya tabbata. Ya fara amfani da wasu lissafe-lissafe dan yin abin da tsari amma sai yaga hakan bazai kaishi ga ci ba, daga nan kawai ya fara sayo kwalayen Ashana yana mannesu da gam guri guda. Hotonnan na sama ya daukeshine lokacin da ashanonin da yake hadawa suka fara bayarda siffar kwallon kuma ya fara murnar burinshi ya kusa cika.
Yaci gaba da manne ashanonin guri guda, duk da cewa aikin akwai wahala amma wahalar bata hanashi ci gaba da ganin ya cimma burinshiba, yace da yana hada ashanunne da daya-daya amma daga baya sai ya rika hada da yawa,kamar guda bakwai ya manne su da gam sannan ya mannasu jikin sauran masu yawan.
Yace da yaje shago siyo ashana sai me shagon yake mai kallon kodai ya tabude, ko kuma zaije ya kona wani bankine? ya kara da cewa amma hakan be dameshi ba yaci gaba da aikinshi.

Yace yana kara manne ashanonin guri guda suna kara bashi siffar kwallo hakan yasashi cikin farin ciki sosai saboda burinshi ya kusa cika.
Yace ashanun suna kara matsewa suna zama kamar kwallo amma sai ya lura ba zasu bashi siffar kwallo sosai irin yanda yake so ba, duk da haka yaci gaba tundadai ya lura zasu hade.
Yace suna kara matsewa, manna ashanun yana kara bashi wahala, domin da suka kusa zama ainihin siffar kwallo, sai ya bi a hankali wajan mamma ashanun dan kada ya bata aikinshi.
Yace yana matukar son wannan hoton domin yana kayatar dashi sosai.
A karshedai ya gama, ashanu sun bashi siffar kwallo, kuma ya rika ajiye kwalayen ashanun dan ya san guda nawa yayi amfani dasu, yace yayi amfani da kwalayen ashana gudaguda dari da arba'in kuma kowane kwali yana da ashana guda dari uku a cikinshi, idan ka hada duka zai baka kwayoyin ashana guda dubu arba'in da biyu kenan. Yace da farko yayi lisaafin zaiyi amfani da kwayoyin ashana guda sama da dubu sittin da biyu ne.

Wannan itace cikakkiyar kwallon Ashana da mutumin ya hada.
A nan mutuminne ya dauko kwallon ashanarshi.
Nan kuma ya kunnawa kwallon ashanar wutane yaci ya cinye.
boredpanda

1 comment:

  1. Wato duk 'kwalwar da bata fahimci Al-Qur'ani ba,kuma bata da Al-Qur'ani to tabbas tana tare da shirme.

    ReplyDelete