Sunday, 4 February 2018

Kasan yawan litattfan dake dakin karatu na me martaba sarkin Kano?

A makon daya gabatane muka ga hotuna daga dakin karatu na me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II wanda yake shake da litattafai iri-iri, a ziyarar da mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya kai jihar Kano jiya, me baiwa shugaban kasa shawara akan sabbin kafafen sadarwa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa ya samu damar shiga dakin karatun na Sarkin.Bashir ya bayyana cewa dakin karatun na da litattafai da yawasu ya kai sama da dubu goma.
Kuma ya bayyana naahi a matsayin daya daga cikin manyan dakunan karatu da ake dasu a Najeriya.
Bashir Ahmad din ne anan yake duba litattafai a dakin karatu na sarkin Kanon.

No comments:

Post a Comment