Tuesday, 20 February 2018

"Ko da APC zata shekara 12 tana mulki ba zata taba kamo PDP a ayyukan raya kasa ba">>Tsohon gwamnan jihar Naija: Babangida Aliyu

Tsohon gwamnan jihar Naija, Babangida Aliyu ya bayyana cewa 'yan jam'iyyar APC na so ya bar PDP dan komawa APC din, ya kara da cewa yasan da hakane bayan da suka rika murna da jin jita-jitar cewa wai ya koma APC din.


Babangida Aliyu ya bayyana cewa shi dan PDP ne na hakika kuma yana da alkibla a siyasarshi saboda haka bazai taba barin jam'iyyar ta PDP ba zuwa wata jam'iyya ba, ya kara da cewa ayyukan da yayi a lokacin yana gwamnane yake birge 'yan APC din shiyasa suke so ya koma cikinsu, kuma yana jaddada musu cewa ko zasu shekara goma sha biyu suna mulki ba zasu taba iya yin irin aikin da PDP tayi ba.

No comments:

Post a Comment