Thursday, 15 February 2018

"Ko yanzu na mutu: Na godewa Allah">>Ummi Zeezee

A wani sako kuma duk na murnar zagayowar ranar haihuwarta, tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta bayyana cewa ita ko yanzu ta mutu ta gode Allah domin ya biya mata bukatunta, tace Allah ya daukakata fiye da yanda take tunani kuma ya tsareta fiye da yanda take tunani haka kuma ya azurtata fiye da nemanta, saboda haka ko yanzu ta mutu Alhamdulillahi.

 
Muna kara tayata murnar zagayowar ranar haihuwarta da fatan Allah ya karo shekaru masu Albarka.

No comments:

Post a Comment