Sunday, 4 February 2018

Kotu ta hana masallaci kiran sallah da lasifika a kasar Jamus

Image result
Wata kotu a kasar Jamus ta hana wani masallaci kiran sallar Juma'a da lasifika dalilin korafin da wasu ma'aurata mabiya addinin kiristanci suka kai mata na cewa kiran sallar yana damunsu kuma abin da ma yafi damunsu shine abinda ake fadi a cikin kiran sallar dake daukaka sunan Allah fiye da abin bautarsu na kiristanci.

Ma'auratan dai suna zaune ne kusan kilomita daya tsakaninsu da masallcin, lamarin ya farune a birnin Oer-Erkenschwick dake kasar ta Jamus. a shekarar 2014, mahukuntan birinin sun baiwa masallacin damar yin amfani da lasifika wajan kiran sallar Juma'a.

Amma shekara daya bayan hakan, sai wadannan ma'aurata suka shigar da kara kotu. Kuma sukayi nasara. wannan hukuncin dai shine irinshi na farko a kasar ta Jamus kamar yanda Daily Mail ta ruwaito, domin kuwa akwai musulmai da masallatai da dama a kasar dake amfani da Lasifika wajan kiran sallah.

Daya daga cikin masu gudanarwa na masallacin da ake kira da Huseyin Turgut ya bayyana cewa hukuncin kotun be mai dadiba, kuma akwai makwautan masallacin na kusa sosai wadanda ba musulmi ba amma basu taba yin irin wannan korafiba.

Kotun dai tace masallacin zai iya fito da wani sabon tsari na kiran sallar amma ba amfani da lasifika ba.

Photo:britannica.com

No comments:

Post a Comment