Friday, 23 February 2018

' Ku bani lokaci inyi tunani'>>Inji shugaba Buhari lokacin da gwamnoni suka ce ya sake tsayawa takarar shugaban kasa

A daren jiyane, gwamnonin jam'iyyar APC sukayi taro da shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda suka rokeshi da ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu.


Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kungiyar gwamnonin APC dinne, gwamnan jihar Imo Rochas ya bayyanawa manema labarai hakan, bayan taron nasu da shugaba Buhari, ya kara da cewa sun cewa shugaba Buharin ya sake tsayawa karane saboda irin ayyukan da yayiwa Najeriya na ci gaba cikin kankanin lokaci.

Saidai shuga Buharin yace musu su bashi lokaci zai yi tunani akan hakan kuma ya fito ya shaidawa Duniya matsayarshi.

No comments:

Post a Comment