Saturday, 17 February 2018

Kungiyar Musulmi ta tallafawa wadanda harin bindigar Amurka ya shafa

Wata kungiyar musulmai a kasar Amurka ta kaddamar da kokon barar tallafawa mutanen da harin da wani tashi yakai da bindiga jihar Florida inda ya kashe mutane 17 da dama kuma suka jikkata, ranar Larabar data gabata.Jim kadan  bayan faruwar lamarin sai wannan kungiya ta musulmai ta bude wani shafin yanar gizo inda ta fara nemawa wadanda abin ya shafa tallafin kudi dan rage musu radadin abinda ya samesu, kungiyar tace manzo tsira, Annabi Muhammad(S. A. W) ya koyar damu kyautatawa makwaucin mu da kuma kula da hakkokinshi.

Wannan abu ba karamin daukar hankalin Duniya yayi ba kuma akai ta yabawa wannan kungiya da ma musulmi baki daya, muna fatan Allah ya taimaki wannan kungiya ya kuma saka musu da Alheri bisa wannan hobbasa da sukayi ta daukaka addinin Allah ta hanya me kyau.

No comments:

Post a Comment