Monday, 19 February 2018

Ma'aikatun gwamnatin tarayya 5 zasu kashe sama da miliyan 221 akan abinci da kayan tande-tande a wannan shekarar

Jumullar kudin da wasu manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya biyar zasu kashe akan abinci da kayan shaye-shaye da tande-tande a wannan shekarar sun kai sama da naira miliyan dari biyu da ashirin da daya, kamar yanda hakan yake bayyane a cikin kasafin kudi na wannan shekarar.


Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ma'aikatun da zasu kashe wadannan makudan kudi akan abinci da kayan sha sune ma'aikatar Watsa labarai da ma'aikatar kudi da ma'aikatar shirya kasafin kudi da tsare-tsare, da ma'aikatar noma.

A hakama wai wasu ma'aikatun ba'a basu kudin abinci ba da shaye-shayen kenan.

No comments:

Post a Comment