Saturday, 10 February 2018

Maciji ya cinye kudin sayar da katin Jamb da yawansu yakai miliyan 36

Wani abin al'ajabi ya faru a Makurdi jihar Benue wanda ya daurewa mutane kai wasu suka rika fadin cewa karyane wasu kuma abin dariya ya basu. Wata ma'aikaciyar hukumar shirya jarabawar shiga jami'a, Jamb ce ta bayyana cewa kudin katin da take sayarwa da dalibai da yawansu yakai miliyan talatin da shida sun bace, kuma wai wani shu'umin macijine ya hadiye kudin.


Matar me suna Philomina Chieshe ta bayyanawa hukumar bincike da aka nada ta binciki yanda kudin suka bata cewa, idan ta sayar da katin jarabawar Jamb takan kai kudin banki amma sai take shan wahala wajan lissafi da bada ba'asin yawan kudin, dalilin hakane yasa ta koma ajiye kudin a gida.

Ta kara da cewa abin al'ajabi shine sai taga kudin suna bacewa a duk lokacin da taje zuba wasu, wannan dalilin yasa ta fara bincike kuma ta gano cewa yarinyar aikin gidanta ce da wani daga cikin ma'aikatar ta Jamb suka hada baki suke sace kudin ta hanyar sihiri inda suke aiko wani maciji yana hadiye kudin.

Matar ta bayyana cewa, me aikin natace da kanta ta gayamata yanda suke satar kudin kuma  itama abin ya bata mamaki sosai.
Dailypost

No comments:

Post a Comment