Monday, 12 February 2018

Macijin daya Hadiyi kudi: Kalli martanin EFCC: An dakatar da ma'aikaciyar da kudin suka bata a hannunta

Labarin ma'aikaciyar hukumar shirya jarabawar shiga Jami'a da aka nemi ba'asin batan kudi miliyan talatin da shida da suka bata a hannunta tace wai maciji ya hadiyesu ya dauki hankulan mutane sosai inda akata bayyana mabanbanta ra'ayoyi, hukumar hana yiwa arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta saka wannan hoton na mikiya tana shirin kashe maciji inda a dandalinta na sada zumunta da muhawara na Twitter kuma ta rubuta cewa, kada ku sassautawa maciji me hadiye kudi.Wannan abu ya daukii hankulan mutane sosai inda waau suka bayyana hakan da matakin daya dace.

Tuni dai rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta dakatar da matar kuma tana fuskantar matakan ladabtarwa da suka dace da laifinta.

No comments:

Post a Comment