Wednesday, 14 February 2018

Madugun adawan kasar Zimbabuwe, Morgan Tsvangirai ya mutu

Tsohon ministan kasar Tsvangirai ya rasu yana da shekaru 65 a duniya bayan fama da cutar sankara wato Cancer sama da shekaru biyu kamar yadda jaridun Zimbabuwe suka tabbatar a shafukansu na twitter, ko da ya ke ciwon ya fi tsanani a kwanaki biyu da suka gabatar bayan da ya ke jinya a Afirka ta Kudu.


Mutuwar jagoran adawan na zama koma baya ga babbar jam'iyar adawa ta MDC ganin saura watanni a gidanta da babban zabe karon farko tun bayan kawarda tsohon shugaban kasar Robert Mugabe a kan mulki.
Dw

No comments:

Post a Comment