Sunday, 11 February 2018

Manyan masana'antar fina-finan Hausa basa so wani ya taso ya fisu>>Ali Artwork

Tauraron me wasan barkwanci na fina-finan Hausa, Ali Artwork ya sake sukar manyan masana'antarsu ta fim din Hausa inda ya zargesu da cewa basu renon yara dan su tashi su zama wani abu, kullun saidai suyi ta yiwa mutum dadin baki.


Ali Artwork ya bayyana cewa duk irin fadan dake faruwa a masana'antar manyan jarumanne suke shiryashi duk shekara dan kada a daina maganarsu.

Ga sakon na Ali Artwork kamar haka:

"Shawara! Shawara!! Shawara!!! Ina kira GA Matasan mu da suke sha'awar shigowa wannan masana'anta ta KANNYWOOD idan mutum zai shigo to yane mi sana'a acikinta kada ka dogara da daya daga cikin wa yan nan mutane da tunanin cewar za su taimake ka tsakani da Allah to ka yaudari kan ka saboda dukkansu yan jari hujjane babu wanda zai taimakeka dan kazama wani abu sai dan kai ta tashi a yaron su in kuma baku gamsu ba to kuduba duk jaruman da suke taimaka wa ya taba zuwa yafisu? daga sunga ka fara tasowa zaka fisu to ananne za suyi ta maka mugunta har sai ka je kasa daga lokacin da ka kula da hakan kai kokarin daukar mataki sai kaji sun fara maka gori suna cewa kai butulune ina so jama'a kudinga kula da hakan wannan rikice-rikicen da kukaga yana faru shiryashi suke duk karshen shekara badan komai ba sai dan kawar da hankulan mutane a kan yaran da suke tasowa saboda suna gudun kar a daina yayinsu dan haka bari suyi abunda za'aita maganar su a media ni da kuke gani na mayar da hankali a kan wasan barkwanci tun daga lokacin da na kula baza su taimakamin ba na koma na dogara GA Allah wasu ma a cikinsu har dariya akemin ana ganin babu inda zanje naci gaba da hakuri a hakan akwana a tashi abun yafara shiga zukatan mutane har na samu a ka turo mun da wani aiki daga Lagos a lokacin nakira yaran daya daga cikinsu don su tayani aiki amma sai ya hanasu yi daya kuma na taba neman alfarma ya mun tallah a lokacin bani da shafukan tallah nanemin zan biyashi a kan ya min tallah amma yaki duk da irin wahalar da nake musu a lokacin sai gashi wata jaruma wanda ban taba yiwa komai ba magana ma ba sosai muke ba wannan jaruma ba kowa bace illa HADIZA GABON inamata magana kan kace me duk sai da tabi shafukanta na yanan gizo tamin tallah cikin ikon Allah sai gashi na samu alkhari sosai kuma batare da ta karbi sisina ba shiyasa da JAMILA NAGUDU da HADIZA GABON ba zan taba mancewa da kuba na gode da alkhari da kukamin da kuma gudun mawar da kuka bani a harkokina don haka ina kiran matasan KANNYWOOD da ku kula da kyau kar ai ta muku dadin baki da yaudara da sunan za a taimakeku har sai lokaci ya kure don haka ku tashi tsaye wallahi YOUNG GENERATION lokacin mune yanzu."

No comments:

Post a Comment