Wednesday, 7 February 2018

"Masu rura wutar rikicin Ali Nuhu da Adam A. Zango ku daina: In ba haka ba zaku ji kunya">>Jakadiyar FKD

Jarumar fina-finan Hausa, Fatima Makamashi, Jakadiyar FKD ta yi kira ga masu rura wautar rikicin dake faruwa a masana'antar fina-finan Hausa ta hanyar zage-zage tsakanin masoyan Ali Nuhu da na Adam A. Zango da cewa subi a hankali domin zasu iya zuwa suji kunya.Fatima ta kara da cewa su duka jaruman da ake magana akansu manyane kuma a iya saninta babu wani abu na sabani dake tsakaninsu. A karshe Fatimar tayi kira ga Alin da Adamu da su kai zuciya nesa kada abinda yaransu keyi yayi tasiri a kansu.


No comments:

Post a Comment