Friday, 2 February 2018

Mata Musulmi sun gudanar da ranar Hijabi ta Duniya

Wasu mata musulmi a Liberia suke gudanar da ranar sanya hijabi
A shekara ta 2013 ne aka kadammar da ranar Hijabi ta mata musulmi wadda ake yi a ranar 1 ga watan Fabareru ta kowace shekara. Wadanda suka shirya ranar kan gayyato mata daga sassa daban -daban na Duniya da kuma addini su sanya hijabi a yinin wannan rana ,domin fadakar da mutane kan muhimancin sanya hijabi da kuma irin wariyar da musulmi mata suke fuskanta a kasashen Duniya da dama.


Wadanda suka gudanar da wannan rana sun rika amfani da hashtag #WorldHijabDay.
Mata musulmi kan fuskanci matsala idan sun sanya hijabi a wasu yankuna na duniya, ko a Nigeria ma an samu wasu batutuwa dangane da kalubalen da matan musulmi suke fuskanta kan hijabi.
A bara an hana wata daliba zama lauya bayan ta kamala karatunta.
Hukumomin makarantar horas da lauyoyi sun ce sun hana Amasa Firdaus shiga cikin taron yaye lauyoyin ne saboda bata sanya tufafin da ya dace ba.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment