Wednesday, 7 February 2018

Mintuna kadan kamin sulhun Ali Nuhu da Adam A. Zango: Ali Artwork yace da gangan jaruman suka shirya wannan rikici dan gwara kan masoyansu

Mintuna kadan kamin sanarwar sulhunta Ali nuhu da Adam A. Zango ta fito, tauraron me wasan barkwanci, Ali Artwork ya zargi jaruman biyu da shirya fadan dake faruwa tsakanin masoyansu da gangan.


Yace su suka shirya abinda ke faruwa kuma a bayama sun taba yin haka, inda ya gargadi masoyansu da cewa subi a hankali in ba haka ba zasu zo su musu dariya, Alin ya kuma zargi jaruman da son ai ta basu girma da kuma rashin biyan mutum cikakken hakkinshi idan ya musu aiki. Adam A. Zango dai ya fara wata fafutuka inda yace zaiyi yaki da masu ahirya fim basa biyan jarumai hakkinsu yanda ya kamata, to gashi labari ya fito daga bakin Ali Artwork cewa shima yana cikinsu.

"
Duk abunda kuka GA sunayi suna sane kuma su suke kirkirar hakan don su motsa jam'iyya kar a ce ai kwana biyu an manta da su to ku sani ku Masoyansu ku suka mayar mahaukata in baku manta ba a shekaru baya suntaba shirya irin wannan rikicin nasu mu kazo mukai ta cecekuce a kai Amma daga Karshe mai hakan ta haifar sai suka maidamu bamu san komai ba Dan haka kusan duk wanda yasa kansa sai yayi dana sani ni yanzu babu ruwana da kowa a cikinsu dan ba wanda a cikinsu zai iya kashe min matsalar dubu 200,000 kowa a cikinsu na zauna da shi ba wanda bai moreniba akan harkata ta editing Amma babu wanda na taba WA aiki ya dauki dubu dari 100,000 ya bani in kuma da akwai ya fito ya karyatani sai dai kai ta bautar banza sun fiso kullum kai ta basu girma suna zalintarka to ku sani anyi walkiya munga kowa #Kyar_Nake_Kallonku ba ruwa na da rigimar wani ni ma takaina nake in kanayi dani inayi da kai in bakayi dani nima baruwa na dakai ku kuma Ali da Adamu duk sanda kuka GA dama ku shirya ku ta dama ni ko a jikina ko kuma mutum ya bar industry din tuda ba da ita aka haifi mutum ba don haka mu zamu ciyar da harkar gaba insha Allah tunda ku kun kasa kullum sai Hassada da muna furci don haka ni na dogara GA Allah shine gatana ba wani MUTUM BA."

No comments:

Post a Comment