Sunday, 4 February 2018

Musa ya koma CSKA Moscow da kafar dama: Har ya ci kwallonshi ta farko

Dan wasan Najeriya, Ahmad Musa dake bugawa kungiyar Leicester ta kasar Ingila wasa da kuma yanzu ya koma tsohuwar kungiyarshi ta CSKA Moscow ta kasar Rasha akan aro, da alama ya koma da kafar dama, domin kuwa a wani wasan sada zumunci da kungiyar ta buga da Nordsjaelland, wanda ya kare 1-1, Musa ya zura kwallonshi ta farko.Kamin komawarshi CSKA Moscown an rika rade-radin cewa Musa zai koma bangaren Laligane da taka leda a matsayin aro.

Bayan wasan, musa ya bayyanawa manema labarai cewa shi ya zabi ya dawo kungiyarshi ta CSKA Moscow, domin kuwa kamar gida take a gurinshi ya san 'yan wasan, kuma yasan yanayin buga kwallonsu.

Musa dai ya dade a Leicester yana dumama benci ba tare da ana sakashi yana buga wasa ba, amma da alama yanzu ya samu dama da tauraruwarshi zata sake haskawa.

No comments:

Post a Comment