Thursday, 22 February 2018

"Na hakura da abinda aka min: Kai daga yau ma duk wanda aka zageni ya ramamin ban yafe mishi ba">>Adam A. Zango

Dazune tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya bayyana cewa tura ta kai bango zai fito ya rama irin abubuwan da ake mishi, to bayan wani dan lokaci sai kuma Adamun ya goge wancan sako na farko daya saka ya kuma bayyana cewa ya hakura da abinda aka mishi din.

 Adamun ya bayyana cewa" Wanda yafi kowa karfi a cikin Al'umma shine wanda aka zalunta kuma yana da karfin daukar mataki amma sai yayi hakuri, zamuci gaba da hakuri don nasan a karshe mune da nasara. Kamar yadda manzon Allah S.A.W yayi umarni. A kara hakuri yan uwa da abokan arziki".

Adamun ya kuma kara da cewa " Daga yau duk wanda ya kara rigima ko hayaniya akan an zageni ko an zagi iyayena a cikin kanne na, abokaina da yarana, Allah ya isa ban yafe masaba."

Haka akeso, Adam A. Zango dai dama a farkon shekararnan ya bayyana cewa za'a rika jinshi akai-akai yana zuwa da sabbin abubuwa, kuma koda a fadan farko daya so ya barke tsakaninshi da Ali Nuhu, me wasan barkwanci, Ali Artwork yace, su manyan ne suka hadashi dan gwara kan yaransu. Muna fatan Allah yasa karshen wannan abu kenan kuma yasa wadanda Adamun ya gayawa wannan magana suji, dan a samu zaman lafiya.

No comments:

Post a Comment