Sunday, 18 February 2018

Namu yayi abin yabo: Bahaushe yayi zarra a Duniya inda ya samar da hanyar maganin makanta mafi sauki

Wani hazikin Bahaushe wanda ya fito daga jihar Katsina me suna, Bashir Dodo yayi abin yabo da Duniya ta jinjina mishi, Bashir ya lashe wata gasar daukar hotunan sassan jikin mutane ce da akeyi dan kawo cigaba a harkar kula da lafiyar 'yan Adam.


Gasar ta wannan shekara da akayi a kasar Portugal, Bashir yazo da wani tsari wanda zai taimaka cikin gaggawa wajan magance ciwon makanta, hakan yasa bashir ya zamo na daya a tsakin dalibai da suka fafata a wannan gasar.

Bashir yayi karatun digirin koli na Dakta a wata jami'ar kasar Ingila.

Muna mishi fatan Alheri da kuma Allah ya kara basira.

No comments:

Post a Comment