Thursday, 15 February 2018

Neymar yasha ruwan Allah wadai saboda nuna rashin da'a a wasan su da Real Madrid

Dan wasan kungiyar PSG, Neymar yasha ruwan Allah wadai daga 'yan kallo saboda irin yanda ya nuna fushinshi da kuma rashin jin dadi a fili bayan da kungiyarshi ta PSG ta kwashi kashinta a hannu daga gun Real Madrid da ce 3-1 a wasan da suka buga na cin kofin zakarun turai, jiya Laraba.Bayan kammala wasandai Neymar bai tsaya gaisawa da 'yan kungiyarshi ta PSG ba ballantana ma 'yan Real Madrid, ya tafi fuska a murtuke ya shige kofar fita daga filin wasan, yayin da sauran 'yan wasa keta gaisawa da juna.

Wannan yasa 'yan kallo suka shiga shafin Twitter suna ta Allah wadai da wannan halayyar da Neymar ya nuna inda da yawa suka fassarata da rashin da'a. Wasu ma har cewa suka rikayi bazai taba zama irin Messi ko Ronaldo ba matukar yaci gaba da nuna irin wannan dabi'ar.
Wasu sunce ai bashi kadai bane dan PSG kuma sauranma sunji ba dadi amma saboda suna idon Duniya suka hadiye.

No comments:

Post a Comment